Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Esta 3:11-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Sa'an nan ya ce masa, “Da kuɗin, da mutanen duk an ba ka, ka yi yadda ka ga dama da su.”

12. Sai aka kirawo magatakardun sarki a rana ta goma sha uku ga watan fari. Bisa ga umarnin Haman aka rubuta doka zuwa ga shugabannin mahukuntai na sarki, da masu mulkin dukan larduna, da sarakunan shugabannin jama'a. Aka rubuta zuwa kowane lardi da irin rubutunsa, da kowaɗanne mutane kuma da harshensu da sunan sarki Ahasurus. Aka hatimce ta da hatimin zoben sarki.

13. Aka ba 'yankada-ta-kwana takardun zuwa dukan lardunan sarki don a hallaka Yahudawa, a karkashe, a ƙarasa su, ƙanana da manya, mata da maza, duk a rana ɗaya, wato ran goma sha uku ga watan goma sha biyu, wato watan Adar, a kuma washe dukiyoyinsu.

14. Sai a ba kowane lardi fassarar dokar, don a yi shelarta ga dukan mutane, su kasance a shirye don ranar.

15. Bisa ga umarnin sarki, sai 'yankada-ta-kwana, suka tafi da sauri. Aka ba da umarni a Shushan, masarauta. Sarki da Haman kuwa suka zauna don su sha, amma birnin Shushan ya ruɗe.

Karanta cikakken babi Esta 3