Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Esta 1:18-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

18. Yau ma matan Farisa da Mediya waɗanda suka ji abin da sarauniya ta yi, haka za su faɗa wa dukan hakimai. Wannan zai kawo raini da fushi mai yawa.

19. Idan sarki ya yarda, bari ya yi doka, a kuma rubuta ta cikin dokokin Farisa da Mediya don kada a sāke ta, cewa Bashti ba za ta ƙara zuwa wurin sarki Ahasurus ba. Bari sarki ya ba da matsayinta na sarauta ga wata wadda ta fi ta.

20. Sa'ad da aka ji dokar sarki, wadda zai yi a dukan babbar ƙasarsa, dukan mata za su girmama mazansu, ƙanana da manya.”

21. Wannan shawara ta gamshi sarki da sauran sarakai, sarki ya yi kamar yadda Memukan ya shawarta.

22. Sai ya aika da takardu zuwa dukan lardunan sarki, kowane lardi da irin rubutunsa, kowaɗanne mutane kuma da harshensu, domin kowane namiji ya zama shugaban gidansa, ya kuma zama mai faɗa a ji.

Karanta cikakken babi Esta 1