Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Esta 1:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ahasurus ya yi sarauta daga Hindu har zuwa Habasha, ya mallaki larduna ɗari da ashirin da bakwai.

2. A waɗannan kwanaki, sarki Ahasurus yake zaune a gadon sarautarsa a Shushan, masarauta.

3. A shekara ta uku ta sarautarsa, sai ya yi biki saboda sarakunansa, da barorinsa, da sarakuna yaƙin Farisa da Mediya, da manyan mutane, da hakiman larduna.

4. Sai ya nuna wadatar mulkinsa, da martabarsa, da darajarsa har kwanaki masu yawa, wato kwana ɗari da tamanin.

5. Bayan da waɗannan kwanaki sun cika, sai sarki ya yi wa manya da ƙanana waɗanda suke a Shushan, wato masarauta, biki, har na kwana bakwai a filin lambun fādar sarki.

Karanta cikakken babi Esta 1