Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Dan 8:16-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. Na kuma ji muryar mutum a gāɓar Ulai ta ce, “Jibra'ilu, ka sa wannan mutum ya gane wahayin.”

17. Don haka sai ya zo kusa da inda nake tsaye. Da ya zo sai na firgita, na faɗi rubda ciki.Amma ya ce mini, “Ɗan mutum, wannan wahayi yana a kan lokaci na ƙarshe ne.”

18. Sa'ad da yake magana da ni, sai barci mai nauyi ya kwashe ni da nake kwance rubda ciki, amma sai ya taɓa ni, ya tashe ni tsaye.

19. Ya ce mini, “Zan sanar da kai abubuwan banhaushi, da za su faru nan gaba, gama wahayin ya shafi ƙayyadadden lokaci na ƙarshe.

20. “Ragon nan mai ƙaho biyu da ka gani, sarakunan Mediya ne da na Farisa.

21. Bunsurun kuwa Sarkin Hellas ne. Babban ƙahon nan da yake tsakanin idanunsa shi ne sarki na farko.

22. Ƙahoni huɗu da suka tsiro bayan karyewar na farin, sarakuna huɗu ne da za su fito daga cikin al'ummarsa, amma ba za su sami iko irin nasa ba.

23. “A wajen ƙarshen mulkinsu, sa'ad da muguntarsu ta kai intaha, wani mugun sarki mai izgili, mayaudari, zai fito.

24. Zai ƙasaita, amma ba ta wurin ikon kansa ba. Zai yi mummunar hallakarwa. Zai hallaka manyan mutane, da tsarkaka. Zai yi nasara cikin abin da zai yi.

25. Ta wurin mugun wayonsa zai sa cin hanci ya haɓaka. Zai ɗaukaka kansa a ransa. Zai hallaka mutane da yawa, ba zato ba tsammani, har ma zai tasar wa Sarkin sarakuna, amma za a hallaka shi ba ta hannun mutum ba.

26. Wannan wahayi na kwanaki wanda aka nuna maka gaskiya ne, asiri ne kuma, kada ka faɗa, gama zai daɗe kafin a yi.”

27. Ni Daniyel kuwa na siƙe, na yi ciwo, har na kwanta 'yan kwanaki, sa'an nan na tashi na ci gaba da aikin sarki. Wahayin ya shige mini duhu, ban gane shi ba.

Karanta cikakken babi Dan 8