Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Dan 6:13-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Sa'an nan suka amsa wa sarki cewa, “Ya sarki, Daniyel ɗin nan, wanda yake ɗaya daga cikin waɗanda aka kwaso daga ƙasar Yahuza, bai kula da kai ba, balle fa dokar da ka kafa, amma yana ta yin addu'a sau uku kowace rana.”

14. Sa'ad da sarki ya ji wannan magana, sai ransa ya ɓaci ƙwarai, sai ya shiga tunani ta yadda zai yi ya kuɓutar da Daniyel. Ya yi ta fama har faɗuwar rana yadda zai yi ya kuɓutar da shi.

15. Sai waɗannan mutane suka zo wurin sarki, suka ce masa, “Ka sani fa ya sarki, doka ce ta Mediya da Farisa, cewa ba dama a soke doka ko umarni wanda sarki ya kafa.”

16. Sarki kuwa ya umarta a kawo Daniyel, a tura shi cikin kogon zakoki. Sarki kuma ya ce wa Daniyel, “Ina fata Allahn nan wanda kake bauta masa kullum zai cece ka.”

17. Sai aka kawo dutse aka rufe bakin kogon, sarki kuwa ya hatimce shi da hatiminsa, da hatimin fādawansa, don kada a sāke kome game da Daniyel.

18. Sarki ya koma fādarsa, ya kwana yana azumi, bai ci abinci ba, ya kuma kāsa yin barci.

19. Gari na wayewa, sai sarki ya tashi, ya tafi da gaggawa wurin kogon zakoki.

20. Da ya zo kusa da kogon da Daniyel yake, sai ya ta da murya ya yi kira da damuwa, ya ce wa Daniyel, “Ya Daniyel, bawan Allah mai rai, ko Allahn nan naka wanda kake bauta masa kullum, yana da ikon cetonka daga zakoki?”

21. Sai Daniyel ya ce wa sarki, “Ran sarki ya daɗe!

22. Allahna ya aiko mala'ikansa ya rufe bakunan zakoki, ba su iya yi mini lahani ba, domin ban yi wa Allah laifi ba, ban kuma yi maka ba.”

23. Sarki ya cika da murna ƙwarai, ya umarta a fito da Daniyel daga kogon. Sai aka fito da Daniyel daga kogon, aka ga ba wani lahani a jikinsa saboda ya dogara ga Allahnsa.

24. Sai sarki ya umarta a kawo mutanen nan da suka yi wa Daniyel maƙarƙashiya, a tura su, da 'ya'yansu, da matansu cikin kogon zakoki. Tun ba su kai ƙurewar kogon ba, sai zakoki suka hallaka su, suka kakkarye ƙasusuwansu gutsi-gutsi.

25. Dariyus sarki kuwa ya rubuta wa dukan jama'a da al'ummai, waɗanda suke zaune a duniya duka, ya ce, “Salama ta yalwata a gare ku.

Karanta cikakken babi Dan 6