Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Dan 6:1-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Dariyus ya ga ya yi kyau ya naɗa muƙaddas guda ɗari da ashirin a dukan mulkinsa.

2. Sai ya naɗa Daniyel da waɗansu mutum biyu su zama shugabannin muƙaddasan nan. Su muƙaddasan kuwa za su riƙa ba shugabannin labarin aikinsu, don kada sarki ya yi hasarar kome.

3. Sai Daniyel ya shahara fiye da sauran shugabannin, da su muƙaddasan, domin yana da nagarin ruhu a cikinsa. Sarki kuwa ya shirya ya gabatar da shi kan dukan mulkin.

4. Sai shugabannin, da su muƙaddasan suka nemi Daniyel da laifi game da ayyukan mulki, amma ba su sami laifin da za su tuhume shi da shi ba, domin shi amintacce ne, ba shi da kuskure ko ha'inci.

5. Sai mutanen nan suka ce, “Ba za mu sami Daniyel da laifin da za mu kama shi da shi ba, sai dai ko mu neme shi da laifi wajen dokokin Allahnsa.”

6. Sa'an nan waɗannan shugabanni da muƙaddasai suka ƙulla shawara, suka zo wurin sarki, suka ce masa, “Ran sarki Dariyus ya daɗe!

7. Dukan shugabannin ƙasar da masu mulki da muƙaddasai, da 'yan majalisa, da wakilai, sun tsai da shawara, cewa ya kamata sarki ya kafa doka, ya yi umarni cewa a cikin kwana talatin nan gaba duk wanda ya yi addu'a ga wani gunki ko mutum, in ba a gare ka ba, ya sarki, sai a tura shi cikin kogon zakoki.

Karanta cikakken babi Dan 6