Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Dan 3:14-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

14. Nebukadnezzar ya ce musu, “Ko gaskiya ne, wai kai Shadrak, da Meshak, da Abed-nego ba ku bauta wa allolina ba, ba ku kuma yi sujada ga gunkin zinariya da na kafa ba?

15. Yanzu, idan kuna so, sa'ad da kuka ji ƙarar ƙaho, da sarewa, da garaya, da goge, da molo, da algaita, da kowane irin abin kaɗe-kaɗe da bushe-bushe, sai ku fāɗi ƙasa, ku yi sujada ga gunkin zinariya da na kafa. Idan kun yi haka, da kyau. Amma idan ba ku yi sujadar ba, nan take za a jefa ku a tanderun gagarumar wuta, in ga ko wane ne allahn nan da zai kuɓutar da ku daga hannuna?”

16. Shadrak, da Meshak, da Abed-nego kuwa suka amsa wa sarki suka ce, “Ya maigirma Nebukadnezzar, ba mu bukatar mu amsa maka da kome a kan wannan al'amari.

17. Idan haka ne, Allahnmu wanda muke bauta wa, yana da iko ya cece mu daga tanderun gagarumar wuta, zai kuwa kuɓutar da mu daga hannunka, ya sarki.

18. Ko ma bai cece mu ba, ka sani fa ya sarki, ba za mu bauta wa allolinka, ko kuma mu yi wa gunkin zinariya da ka kafa sujada ba.”

19. Sai Nebukadnezzar ya husata ƙwarai da Shadrak, da Meshak, da Abed-nego, har fuskarsa ta sāke. Sai ya umarta a ƙara zuga wutar, har sau bakwai fiye da yadda take a dā.

Karanta cikakken babi Dan 3