Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Dan 12:6-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Dayansu ya ce wa mutumin da yake sāye da rigar lilin, wanda yake tsaye a gaɓar kogin, “Sai yaushe waɗannan abubuwan banmamaki za su ƙare?”

7. Sai mutumin da yake sāye da rigar lilin ɗin, wanda yake tsaye a gaɓar kogin ya ɗaga hannuwansa sama, sa'an nan ya rantse da wanda yake rayayye har abada, ya ce, “Za a yi shekara uku da rabi. Za a kammala waɗannan abubuwa, sa'ad da aka gama ragargaje ikon tsarkakan mutane.”

8. Na ji, amma ban gane ba. Sai na ce, “Ya shugabana, mene ne ƙarshen waɗannan abubuwa?”

9. Sai ya ce, “Yi tafiyarka, Daniyel, gama an rufe wannan magana, an kuma kulle ta har ƙarshen lokaci.

Karanta cikakken babi Dan 12