Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Dan 11:15-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. Sa'an nan sarkin arewa zai zo ya gina mahaurai a jikin garun birni don ya ci birnin da yaƙi. Sojojin kudu kuwa ba za su iya tsayawa ba, ko zaɓaɓɓun jarumawansa ma, gama za su rasa ƙarfin tsayawa.

16. Amma wanda ya kawo masa yaƙin zai yi yadda ya ga dama, ba wanda zai iya ja da shi. Zai tsaya a ƙasa mai albarka, ya mallake ta duka.

17. Zai yunƙuro da dukan ƙarfin mulkinsa, zai zo ya gabatar da shawarar salama, ya aikata ta. Zai aurar masa da 'yarsa don ta lalatar da mulkin abokin gabansa, amma wannan dabara ba za ta ci ba.

18. Daga nan zai yunƙura zuwa ƙasashen gaɓar teku, ya ci da yawa daga cikinsu, amma wani jarumi zai kawo ƙarshen fāɗin ransa. Zai sa fāɗin ransa ya koma masa.

19. Sa'an nan zai juya, ya nufi kagarar ƙasarsa, amma zai yi tuntuɓe, ya fāɗi, ba za a ƙara ganinsa ba.”

20. “Wani sarki zai ɗauki matsayinsa, zai aiki mai karɓar haraji cikin daularsa, amma ba da daɗewa ba za a kashe shi, ba cikin hargitsin yaƙi ba.

21. “Wani kuma rainanne zai maye gurbin wancan, shi kuwa ba ɗan jinin sarauta ba ne. Zai taso ba zato ba tsammani, ya ƙwace sarautar ta hanyar zamba.

22. Zai shafe rundunonin sojoji har da rantsattsen shugaba.

23. Daga lokacin da aka ƙulla yarjejeniya da shi, zai yi munafunci. Zai sami iko ta wurin goyon bayan mutane kima.

Karanta cikakken babi Dan 11