Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ayu 42:11-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Sa'an nan dukan 'yan'uwan Ayuba mata da maza da dukan waɗanda suka san shi a dā, suka zo gidansa suka ci abinci tare da shi, suka yi juyayin abin da ya same shi, suka ta'azantar da shi,saboda dukan wahalar da Ubangiji ya aukar masa. Kowannensu ya ba shi 'yan kuɗi da zoben zinariya.

12. Ubangiji ya sa wa wannan zamani na Ayuba albarka, har fiye da na farko. An ba shi tumaki dubu goma sha huɗu (14,000), da raƙuma dubu shida (6,000), da takarkari dubu biyu (2,000), da jakai mata dubu ɗaya (1,000).

13. Ya kuma haifi 'ya'ya maza bakwai, mata uku.

14. Ya raɗa wa ta farin suna Yemima, da ta biyun Keziya,da ta ukun Keren-Haffuk.

15. Duk ƙasar ba 'yan mata kyawawa kamar 'ya'yan Ayuba. Mahaifinsu kuwa ya ba su gādo tare da 'yan'uwansu maza.

16. Ayuba ya rayu shekara ɗari da arba'in bayan wannan, ya ga 'ya'yansa, ya ga jikokin jikokinsa har tsara ta huɗu.

17. Sa'an nan Ayuba ya rasu da kyakkyawan tsufa.

Karanta cikakken babi Ayu 42