Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ayu 39:4-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. 'Ya'yansu sukan yi ƙarfi su girma a fili cikin saura,Sukan yi tafiyarsu ba su komawa wurin iyayensu.

5. “Wa ya bar jakin jeji ya yi yadda yake so?Wa ya ɓalle dabaibayin jaki mai sauri,

6. Wanda na ba fili fetal ya zama gidansa,Da ƙasa mai gishiri a wurin zamansa?

7. Yakan yi wa hayaniyar birane ba'a,Ba ruwansa da tsawar masu kora.

8. Tsaunukan duwatsu ne wurin kiwonsa,A can yake neman kowane ɗanyen abu.

9. “Kutunkun ɓauna zai yarda ya yi maka aiki?Zai yarda ya kwana ɗaya a dangwalinka?

10. Ka iya ɗaure shi da igiya a kwarin kunya?Ko kuwa zai yi maka kaftu a fadamarka?

11. Za ka dogara gare shi saboda tsananin ƙarfinsa?Za ka kuma bar masa aikinka?

12. Ka gaskata zai komo,Ya kawo maka hatsi a masussukarka?

13. “Jimina takan karkaɗa fikafikanta da alfarma!Amma ba su ne gashin fikafikan ƙauna ba.

14. Jimina takan bar wa ƙasa ƙwayayenta,Ta bar ƙasa ta ɗumama su.

15. Takan manta wani ya iya taka su su fashe,Ya yiwu kuma wani naman jeji ya tattake su.

16. Takan yi wa 'ya'yanta mugunta,Sai ka ce ba nata ba ne,Ko da yake ta sha wahala a banza,Duk da haka ba ta damu ba.

17. Gama Allah bai ba ta hikima ba,Bai kuwa ba ta fahimi ba.

Karanta cikakken babi Ayu 39