Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ayu 34:7-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. “Wane irin mutum ne kai, Ayuba,Da kake shan raini kamar yadda kake shan ruwa,

8. Wanda yake cuɗanya da ƙungiyar masu aikata laifi,Kana yawo tare da mugaye?

9. Gama ka ce, ‘Bai amfana wa mutum kome baYa yi murna da Allah.’

10. “Saboda haka ku kasa kunne gare ni, ku da kuke haziƙai,Sam, Allah ba mai aikata mugunta ba ne,A wurin Mai Iko Dukka ba kuskure,

11. Gama bisa ga aikin mutum yake sāka masa,Yana sa aniyarsa ta bi shi.

12. Gaskiya ce, Allah ba zai aikata mugunta ba,Mai Iko Dukka ba zai kauce wa adalci ba.

13. Wa ya shugabantar da shi a kan duniya?Wa ya mallakar masa da duniya duka?

14. Da zai amshe ruhu da numfashin da ya hura wa mutum,

15. Da duk mai rai ya halaka,Mutum kuma ya koma ƙura.

Karanta cikakken babi Ayu 34