Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ayu 30:18-31 Littafi Mai Tsarki (HAU)

18. An yi mini kamun kama-karya,An ci wuyan rigata.

19. Allah ya jefar da ni cikin laka,Na zama kamar ƙura ko toka,

20. “Na yi kira gare ka, ya Allah, amma ba ka amsa mini ba,Na yi addu'a kuma, amma ba ka kula da ni ba.

21. Ka zama mugu a gare ni,Da ƙarfin dantsenka ka tsananta mini.

22. Ka jefa ni cikin guguwa, ka sa ni in hau ta,Ka yi ta shillo da ni cikin rugugin hadiri.

23. Hakika na sani za ka kai ni ga mutuwa,Gidan da aka ƙaddara wa kowane mai rai.

24. “Ashe, wanda yake gab da gagarumar hallaka,Ba zai miƙa hannu ya roƙi taimako a masifar da yake sha ba?

25. Ashe, ban yi kuka saboda wanda yake shan wahala ba?Ashe, ban yi ɓacin rai saboda matalauta ba?

26. Amma sa'ad da na sa zuciya ga alheri, sai ga mugunta,Sa'ad da nake jiran haske, sai ga duhu ya zo.

27. Zuciyata tana tafasa, ba ta kwanciya,Kwanakin wahala sun auko mini.

28. Na yanƙwane, amma ba yanƙwanewar rana ba,Na tsaya a gaban taron jama'a, ina roƙon taimako.

29. “Na zama ɗan'uwan dila,Na kuma zama aminin jiminai.

30. Fatata ta takura, ta zama baƙa,Ƙasusuwana suna zogi saboda zafi,

31. Saboda haka garayata ta zama ta makoki,Sarewata kuma ta zama muryar masu kuka.”

Karanta cikakken babi Ayu 30