Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ayu 30:13-28 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Sun datse hanyata,Sun jawo mini bala'i,Ba kuwa wanda ya hana su.

14. Sun kutsa kamar waɗanda suka karya doka,Sun auka mini da dukan ƙarfinsu kamar yadda suka yi nufi.

15. Sun firgita ni,Sun kori darajata kamar da iska,Wadatata kuma ta shuɗe kamar girgije.

16. “Yanzu zuciyata ta narkeKwanakin wahala sun same ni.

17. Da dare ƙasusuwana karkaɗuwa suke,Azaba tana ta gaigayata ba hutawa.

18. An yi mini kamun kama-karya,An ci wuyan rigata.

19. Allah ya jefar da ni cikin laka,Na zama kamar ƙura ko toka,

20. “Na yi kira gare ka, ya Allah, amma ba ka amsa mini ba,Na yi addu'a kuma, amma ba ka kula da ni ba.

21. Ka zama mugu a gare ni,Da ƙarfin dantsenka ka tsananta mini.

22. Ka jefa ni cikin guguwa, ka sa ni in hau ta,Ka yi ta shillo da ni cikin rugugin hadiri.

23. Hakika na sani za ka kai ni ga mutuwa,Gidan da aka ƙaddara wa kowane mai rai.

24. “Ashe, wanda yake gab da gagarumar hallaka,Ba zai miƙa hannu ya roƙi taimako a masifar da yake sha ba?

25. Ashe, ban yi kuka saboda wanda yake shan wahala ba?Ashe, ban yi ɓacin rai saboda matalauta ba?

26. Amma sa'ad da na sa zuciya ga alheri, sai ga mugunta,Sa'ad da nake jiran haske, sai ga duhu ya zo.

27. Zuciyata tana tafasa, ba ta kwanciya,Kwanakin wahala sun auko mini.

28. Na yanƙwane, amma ba yanƙwanewar rana ba,Na tsaya a gaban taron jama'a, ina roƙon taimako.

Karanta cikakken babi Ayu 30