Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ayu 30:1-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. “Amma yanzu waɗanda na girme su, sai ba'a suke mini,Waɗanda iyayensu maza ba su fi karnukan da suke kiwon garken tumakina ba.

2. Wace riba zan samu ta wurin ƙarfin hannuwansu waɗanda ba su da sauran kuzari?

3. Saboda rashi da matsananciyar yunwa sun rame,Sai gaigayar ƙasa suke yi da dare, a cikin kufai.

4. Sukan tsinki ganyaye masu ɗaci na jeji su ci,Sukan ci doyar jeji.

5. Aka kore su daga cikin mutane,Suka yi ta binsu da ihu kamar yadda ake yi wa ɓarawo,

6. Sai a kwazazzabai suke zamaDa a ramummuka da kogwannin duwatsu.

7. Suka yi ta kuka a jeji,Suka taru wuri ɗaya a cikin sarƙaƙƙiya.

8. Mutane ne marasa hankali marasa suna!Aka kore su daga ƙasar.

9. “Yanzu na zama abin waƙa gare su,Abin ba'a kuma a gare su.

10. Suna ƙyamata, guduna suke yi,Da ganina, sai su tofa mini yau.

11. Domin Allah ya katse lakata, ya ƙasƙanta ni,Saboda haka sun raba ni da zuriyata,

12. A hannun dama 'yan tā da zaune tsaye sun taso mini,Sun runtume ni, sun tura ni a hanyarsu ta hallakarwa.

Karanta cikakken babi Ayu 30