Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ayu 24:13-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. “Akwai mugaye waɗanda suke ƙin haske,Ba su fahimce shi ba, suka ƙi bin hanyarsa.

14. Da asuba mai kisankai yakan fita ya kashe matalauci,Da dare kuma ya yi fashi.

15. Mazinaci yakan jira sai da magariba,Sa'an nan ya ɓoye fuskarsa don kada a gane shi.

16. Da dare ɓarayi sukan kutsa kai cikin gidaje,Amma da rana sukan ɓuya, su guje wa haske.

17. Gama tsananin duhu kamar safiya yake gare su,Sun saba da razanar duhu.

18. “Rigyawa takan ci mugun mutum,Ƙasar da ya mallaka kuwa tana ƙarƙashin la'anar Allah.Ba ya kuma iya zuwa aiki a gonar inabinsa.

19. Kamar dusar ƙanƙara take a lokacin zafi da a lokacin fari,Haka mai zunubi yakan shuɗe daga ƙasar masu rai.

20. Ba wanda zai tuna da shi,mahaifiyarsa ma ba za ta lura da shi ba.Tsutotsi sukan ci shi su hallaka shi sarai.Za a sare mugunta kamar itace.

21. Haka yake samun wanda ya wulakanta gwauraye.Bai kuma nuna alheri ga matan da ba su haihu ba.

22. Allah, da ikonsa, yakan hallaka masu ƙarfi,Allah yakan aikata, sai mugun mutum ya mutu.

23. Ya yiwu Allah ya bar shi ya yi zamansa lafiya,Amma a kowane lokaci zai sa ido a kansa.

24. Mugun mutum yakan ci nasara ɗan lokaci,Daga nan sai ya yi yaushi kamar tsiro,Ya yi yaushi kamar karan dawa da aka yanke.

25. Akwai wanda zai iya cewa, ba haka ba ne?Akwai wanda zai tabbatar da cewa kalmomina ba gaskiya ba ne?”

Karanta cikakken babi Ayu 24