Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ayu 22:24-30 Littafi Mai Tsarki (HAU)

24. Ka jefar da zinariyarka, zinariyarka mafi kyau,Ka jefar da ita kamar dutse ko ƙura.

25. Bari Allah Mai Iko Dukka ya zama zinariyarka,Ya zama azurfa, wadda aka tula dominka.

26. Sa'an nan za ka dogara ga Allah kullayaumin,Ka kuma tarar shi ne asalin farin cikinka.

27. Sa'ad da ka yi addu'a zai amsa maka,Za ka kuwa kiyaye alkawaran da ka yi.

28. Za ka yi nasara a kowane abu da za ka yi,Haske kuma zai haskaka hanyarka.

29. Allah yakan ƙasƙantar da mai girmankai,Yakan ceci mai tawali'u.

30. Zai ceci wanda yake da laifi,Idan abin da kake yi daidai ne.”

Karanta cikakken babi Ayu 22