Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ayu 22:16-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. Kafin ma su kai ga kwanakinsu,Sai rigyawa ta shafe su.

17. Su ne mutanen da suka ƙi Allah,Suka kuwa gaskata ba shi da ikon yi musu kome,

18. Ko da yake Allah ne ya arzuta su.Ba na iya gane tunanin mugaye.

19. Mutanen kirki suna murna,Marasa laifi kuma suna dariyaSa'ad da suka ga ana hukunta mugaye.

20. Duk abin da mugu ya mallaka ya hallaka,Wuta kuwa ta lashe kowane abu da ya ragu.

21. “Yanzu fa, Ayuba, sai ka yi sulhu da Allah,Ka daina ɗaukarsa kamar maƙiyinka,In ka yi haka, to, za ka sami albarka.

22. Ka karɓi koyarwar da yake yi,Ka riƙe kalmominsa a zuciyarka.

23. Hakika sai ka yi tawali'u, ka koma wurin Allah,Ka kawar da dukan muguntar da ake yi a gidanka.

24. Ka jefar da zinariyarka, zinariyarka mafi kyau,Ka jefar da ita kamar dutse ko ƙura.

25. Bari Allah Mai Iko Dukka ya zama zinariyarka,Ya zama azurfa, wadda aka tula dominka.

26. Sa'an nan za ka dogara ga Allah kullayaumin,Ka kuma tarar shi ne asalin farin cikinka.

27. Sa'ad da ka yi addu'a zai amsa maka,Za ka kuwa kiyaye alkawaran da ka yi.

Karanta cikakken babi Ayu 22