Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ayu 22:10-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Don haka ne yanzu akwai ramummuka ko'ina kewaye da kai,Tsoro ya kama ka nan da nan.

11. An yi duhu ƙwarai, har ba ka iya gani,Rigyawa ta sha kanka.

12. “Ashe, ba a can saman sammai Allah yake zaune ba?Sai ya sunkuya ya dubi taurari, ko da yake suna can sama ne.

13. Duk da haka ka ce, ‘Allah bai san kome ba.Gizagizai sun lulluɓe shi, ƙaƙa zai iya yi mana shari'a?’

14. Kana tsammani gizagizai masu duhu sun hana shi gani,A lokacin da yake tafiya a kan iyakar da take tsakanin duniya da sararin sama.

15. “Ka ɗauka a ranka ka bi gurbin da mugaye suke bi kullum?

16. Kafin ma su kai ga kwanakinsu,Sai rigyawa ta shafe su.

17. Su ne mutanen da suka ƙi Allah,Suka kuwa gaskata ba shi da ikon yi musu kome,

18. Ko da yake Allah ne ya arzuta su.Ba na iya gane tunanin mugaye.

19. Mutanen kirki suna murna,Marasa laifi kuma suna dariyaSa'ad da suka ga ana hukunta mugaye.

20. Duk abin da mugu ya mallaka ya hallaka,Wuta kuwa ta lashe kowane abu da ya ragu.

21. “Yanzu fa, Ayuba, sai ka yi sulhu da Allah,Ka daina ɗaukarsa kamar maƙiyinka,In ka yi haka, to, za ka sami albarka.

Karanta cikakken babi Ayu 22