Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ayu 16:2-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. “Ai, na taɓa jin magana irin wannan,Ta'aziyyar da kake yi azaba ce kawai.

3. Ka dinga yin magana ke nan har abada?A kullum maganarka ita ce dahir?

4. In da a ce a matsayina kake, ni kuma ina a naka,Ina iya faɗar duk abin da kake faɗa yanzu.Da sai in kaɗa kaina da hikima,In dulmuyar da kai a cikin rigyawar maganganu.

5. Da sai in ba ka shawara ta ƙarfafawa,In yi ta yi maka maganar ta'azantarwa.

6. “Amma ba abin da zan faɗa wanda zai taimaka,Yin shiru kuma ba zai raba ni da azaba ba.

7. Ka gajiyar da ni, ya Allah,Ka shafe iyalina.

8. Ka kama ni, kai maƙiyina ne.Na zama daga fata sai ƙasusuwa,Mutane suka ɗauka, cewa wannan ya tabbatar ni mai laifi ne.

9. Allah ya kakkarya gaɓoɓina da fushinsa,Yana dubana da ƙiyayya.

10. Mutane sun buɗe baki don su haɗiye niSuna kewaye ni suna ta marina.

11. Allah ya bashe ni ga mugaye.

12. Dā ina zamana da salama,Amma Allah ya maƙare ni,Ya fyaɗa ni ƙasa ya ragargaza ni.Allah ya maishe ni abin bārata.

Karanta cikakken babi Ayu 16