Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ayu 16:15-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. “Ina makoki saye da tsummoki,Ina zaune cikin ƙura a kunyace.

16. Na yi ta kuka har fuskata ta zama ja wur,Idanuna kuma suka yi luhuluhu.

17. Amma ban yi wani aikin kama-karya ba,Addu'ata ga Allah kuwa ta gaskiya ce.

18. “Duniya, kada ki ɓoye laifofin da aka yi mini!Kada ki yi shiru da roƙon da nake yi na neman adalci!

19. Akwai wani a SamaWanda zai tsaya mini ya goyi bayana.

20. Ina so Allah ya ga hawayena,Ya kuma ji addu'ata.

21. “Ina so wanda zai yi roƙo ga Allah domina,Kamar yadda mutum yakan yi roƙo domin abokinsa.

22. Yanzu shekaruna wucewa suke yi,Ina bin hanyar da ba a komawa.”

Karanta cikakken babi Ayu 16