Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ayu 14:15-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. Sa'an nan za ka yi kira, ni kuwa zan amsa,Za ka yi murna da ni, ni talikinka.

16. Sa'an nan za ka lura da kowace takawataAmma ba za ka bi diddigin zunubaina ba.

17. Za ka soke zunubaina ka kawar da su,Za ka shafe dukan kurakuran da na taɓa yi.

18. “Lokaci na zuwa sa'ad da duwatsu za su fāɗi,Har ma za a kawar da duwatsun bakin teku.

19. Ruwa zai zozaye duwatsu, su ragu,Ruwan sama mai ƙarfi zai kwashe jigawa,Kai ma ka bar mutane, ba su da sauran sa zuciya ko kaɗan.

20. Ka fi ƙarfin mutum, ka kore shi har abada,Fuskarsa ta rikiɗe sa'ad da ya mutu.

21. 'Ya'yansa maza za su sami girma,amma sam, ba zai sani ba,Sam, ba wanda zai faɗa masa sa'ad da aka kunyatar da su.

22. Ciwon jikinsa da ɓacin zuciyarsa kaɗai yake ji.”

Karanta cikakken babi Ayu 14