Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Amos 9:1-3 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Na ga Ubangiji na tsaye a wajen bagade. Ya yi umarni, ya ce,“Bugi ginshiƙan Haikali don shirayiduka yă girgiza.Farfasa su, su fāɗi a kan mutane!Sauran mutane kuwa,Zan kashe su a wurin yaƙi.Ba wanda zai tsere, ko ɗaya.

2. Ko da za su nutsa zuwa lahira,Zan kama su.Ko sun hau Sama,Zan turo su.

3. Ko da za su hau su ɓuya a bisaƙwanƙolin Dutsen Karmel,Zan neme su in cafko su.Ko da za su ɓuya mini a ƙarƙashinteku,Sai in sa dodon ruwa yă yayyage su.

Karanta cikakken babi Amos 9