Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Amos 5:20-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

20. Ranar Ubangiji za ta kawo baƙinciki,Ba murna ba.Rana ce ta damuwa ba ta fara'a ba.

21. Ubangiji ya ce,“Na ƙi bukukuwanku na addini.Ina ƙyamarsu!

22. Sa'ad da kuka kawo mini hadayunƙonawaDa hadayunku na tsaba, ba zankarɓa ba.Ba kuma zan karɓi turkakkundabbobinkuWaɗanda kuka miƙa mini hadayungodiya ba.

23. Ku yi shiru da yawan hargowarwaƙoƙinku.Ba na so in saurari kaɗe-kaɗenku dabushe-bushenku.

24. Sai ku sa adalci da nagarta su gudanoa yalwaceKamar kogin da ba ya ƙafewa.

25. “Ya ku, jama'ar Isra'ila, ai, a waɗannan shekaru arba'in da kuka yi cikin jeji kuka kawo mini sadaka da hadayu,

26. duk da haka, kuka ɗauki siffofin gumakanku na taurari, wato Sakkut da Kaiwan, waɗanda kuka yi wa kanku.

27. Ni kuwa zan sa ku yi ƙaura zuwa wata ƙasa gaba da Dimashƙu.” Ubangiji, Allah Mai Runduna, shi ne ya faɗa.

Karanta cikakken babi Amos 5