Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Tar 8:1-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. A ƙarshen shekara ashirin waɗanda Sulemanu ya yi yana gina Haikalin Ubangiji da fādarsa,

2. sa'an nan ya sāke giggina biranen da Hiram ya ba shi, ya zaunar da Isra'ilawa a cikinsu.

3. Sai Sulemanu ya tafi ya ci Hamat-zoba da yaƙi.

4. Sa'an nan ya gina Tadmor a jeji, a Hamat kuwa ya gina biranen ajiya.

5. Ya kuma gina Bet-horon ta kan tudu da Bet-horon ta kwari, birane masu kagara kuwa ya gina musu garu, da ƙofofi, da ƙyamare,

6. da kuma Ba'alat da dukan biranen ajiya waɗanda yake da su, da birane don karusansa, da birane don mahayan dawakansa, ya gina dukan abin da yake bukata a Urushalima, da Lebanon, da a dukan ƙasashen da suke cikin mulkinsa.

7. Dukan jama'ar da suka ragu a ƙasar, wato Hittiyawa, da Amoriyawa, da Ferizziyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa, waɗanda Isra'ilawa ba su hallaka ba,

8. daga cikin zuriyarsu waɗanda suka ragu a ƙasar a bayansu, waɗanda Isra'ilawa ba su hallaka ba, su ne Sulemanu ya tilasta su biya gandu, haka kuwa suke har wa yau.

9. Amma Sulemanu bai bautar da kowa daga cikin mutanen Isra'ila ba, su ne mayaƙansa, da shugabannin yaƙi, da shugabannin karusansa, da mahayan dawakansa.

Karanta cikakken babi 2 Tar 8