Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Tar 6:1-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sulemanu ya ce,“Ubangiji ya riga ya faɗa zai zauna a cikin girgije mai duhu.

2. Yanzu kuwa na gina maka ƙasaitaccen ɗaki,Na gina maka wurin da za ka zauna har abada.”

3. Sa'an nan sarki ya juya, ya dudduba, ya sa wa dukan taron jama'ar Isra'ila albarka, dukansu kuwa suka tsaya.

4. Sai ya ce, “Ubangiji Maɗaukaki ne, Allah na Isra'ila wanda ya yi wa tsohona Dawuda alkawari, ga shi kuwa ya cika shi, gama ya ce,

5. ‘Tun daga ranar da na fito da jama'ata daga ƙasar Masar, ban zaɓi wani birni daga cikin dukan kabilan Isra'ila ba, inda zan gina wurin da sunana zai kasance, ban kuma zaɓi wani mutum da zai shugabanci jama'ata Isra'ila ba.

6. Amma na zaɓi Urushalima domin sunana ya kasance a wurin, na kuma zaɓi Dawuda ya zama shugaban jama'ata Isra'ila.’

7. “Ya zama kuwa tsohona Dawuda ya yi niyyar gina Haikali domin sunan Ubangiji, Allah na Isra'ila.

8. Amma Ubangiji ya ce wa ubana Dawuda, ya kyauta, tun da yake ya yi niyya a zuciyarsa zai gina ɗaki saboda sunansa.

9. Duk da haka, ba shi zai gina Haikalin ba, ɗansa wanda za a haifa masa, shi ne zai gina Haikalin domin sunansa.

Karanta cikakken babi 2 Tar 6