Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Tar 34:1-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Yosiya yana da shekara takwas sa'ad da ya ci sarauta. Ya yi mulki shekara talatin da ɗaya a Urushalima.

2. Ya aikata abin da yake daidai a gaban Ubangiji, yana bin al'amuran da kakansa Dawuda ya yi, bai kauce dama ko hagu ba.

3. A shekara ta takwas ta mulkinsa, a lokacin yana yaro, sai ya fara neman Allah na kakansa Dawuda. A shekara ta goma, sha biyu, sai ya fara tsarkake Yahuza da Urushalima daga masujadai, da Ashtarot, da sassaƙaƙƙun siffofi, da siffofi na zubi.

4. Sai suka farfashe bagadai na Ba'al a gabansa, ya kuma tumɓuke bagadan ƙona turare waɗanda suke a bisansu. Ya ragargaza Ashtarot, da sassaƙaƙƙun siffofi, da na zubi, ya maishe su ƙura. Ya barbaɗa su a kan kaburbura waɗanda suka miƙa hadayu a kansu.

5. Ya kuma ƙone ƙasusuwan firistoci a bisa bagadansu, ya tsarkake Yahuza da Urushalima.

6. A biranen Manassa, da na Ifraimu, da na Saminu, har zuwa Naftali, a kangwayensu kewaye da su,

7. ya farfashe bagadai, ya buge Ashtarot da siffofi, ya maishe su gari, ya tumɓuke dukan bagadan ƙona turare a dukan ƙasar Isra'ila, sa'an nan ya koma Urushalima.

8. A shekara ta goma sha takwas ta mulkinsa, bayan da ya gama tsarkake ƙasar, da Haikalin, sai ya aiki Shafan ɗan Azaliya, da Ma'aseya mai mulkin birnin, da Yowa ɗan Yowahaz, wanda suke magatakarda domin su gyara Haikalin Ubangiji Allahnsa.

Karanta cikakken babi 2 Tar 34