Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Tar 33:1-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Manassa yana da shekara goma sha biyu sa'ad da ya ci sarauta. Ya yi shekara hamsin da biyar yana mulki a Urushalima.

2. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji, ya yi irin ayyukan banƙyama da al'ummai waɗanda Ubangiji ya kore su a gaban jama'ar Isra'ila suke yi.

3. Gama ya sāke giggina masujadai waɗanda Hezekiya, tsohonsa, ya rurrushe. Ya kakkafa bagadai don Ba'al, ya kuma yi Ashtarot. Ya yi sujada ga dukan rundunar sama, ya bauta musu.

4. Ya kuma giggina bagadai a cikin Haikalin Ubangiji inda Ubangiji ya ce, “A Urushalima sunana zai kasance har abada.”

5. Ya giggina bagadai ga dukan rundunar sama a farfajiyan nan biyu na cikin Haikalin Ubangiji.

6. Ya miƙa 'ya'yansa maza hadaya ta ƙonawa a kwarin ɗan Hinnom. Ya yi bokanci, ya yi duba, ya yi tsubbu, yana kuma sha'ani da makarai da mayu. Ya aikata mugunta ƙwarai a gaban Ubangiji, yana tsokanar fushin Ubangiji.

7. Sai ya kafa gunkin da ya yi a cikin Haikalin Allah, wanda Allah ya faɗa wa Dawuda da ɗansa Sulemanu ya ce, “A cikin wannan Haikali da a Urushalima, inda na zaɓa daga cikin dukan kabilan Isra'ila, zan sa sunana har abada.

8. Ba zan ƙara fitar da Isra'ila daga ƙasar da na ba kakanninku ba, in dai sun lura, sun kiyaye, sun aikata dukan abin da na umarce su, da dukan shari'a, da dokoki, da ka'idodi da aka bayar ta hannun Musa.”

9. Ta haka kuwa Manassa ya lalatar da Yahuza da mazaunan Urushalima. Suka aikata muguntar da ta fi ta al'umman da Ubangiji ya hallaka a gaban jama'ar Isra'ila.

10. Ubangiji fa ya yi magana da Manassa da jama'arsa, amma ba wanda ya kula.

11. Saboda haka Ubangiji ya sa sarakunan yaƙi na Sarkin Assuriya su kamo Manassa da ƙugiyoyi, su ɗaure shi da sarƙoƙin tagulla, su kai shi Babila.

12. Amma sa'ad da yake wahala, sai ya roƙi jinƙan Ubangiji Allahnsa, ya ƙasƙantar da kansa sosai a gaban Allah na kakanninsa.

13. Sa'ad da ya yi addu'a gare shi, Allah ya karɓi roƙonsa da hurwarsa, ya sāke komar da shi Urushalima da mulkinsa. Sa'an nan ne Manassa ya sani Ubangiji shi ne Allah.

14. Bayan haka sai ya gina garu a bayan garin Dawuda a yammacin Gihon, a kwari har zuwa Ƙofar Kifi, ya kewaye da shi zuwa Ofel, ya gina shi da tsayi sosai. Sa'an nan ya sa sarakunan yaƙi a garuruwa masu garu na Yahuza.

Karanta cikakken babi 2 Tar 33