Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Tar 30:1-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sai Hezekiya ya aika zuwa ga dukan Isra'ila da Yahuza, ya kuma rubuta wasiƙu zuwa ga Ifraimu, da Manassa, cewa sai su zo Haikalin Ubangiji a Urushalima, domin su yi Idin Ƙetarewa na Ubangiji Allah na Isra'ila.

2. Gama sarki da sarakunansa da dukan majalisar da take a Urushalima sun tsai da shawara a yi Idin Ƙetarewa a wata na biyu,

3. gama ba su iya yinsa a lokacinsa ba, saboda yawan firistocin da suka tsarkake kansu bai isa ba, mutane kuma ba su taru a Urushalima ba.

4. A ganin sarki da na jama'a duka, shirin ya yi daidai.

5. Sai suka ba da umarni a yi shela a Isra'ila duka, tun daga Biyer-sheba, har zuwa Dan, cewa sai mutane su zo Idin Ƙetarewa na Ubangiji Allah na Isra'ila a Urushalima, gama jama'a mai yawan gaske ba su zo wurin yin idin kamar yadda aka umarta ba.

6. Sai mazanni suka tafi ko'ina da ina a dukan ƙasar Isra'ila da ta Yahuza da wasiƙu daga wurin sarki da sarakunansa, yadda sarki ya umarta.“Ya ku jama'ar Isra'ila, ku komo wurin Ubangiji Allah na Ibrahim, da Ishaku, da Isra'ila domin ya sāke juyowa zuwa ga sauranku, waɗanda kuka kuɓuta daga hannun sarakunan Assuriya.

7. Kada fa ku zama kamar kakanninku ko 'yan'uwanku, marasa bangaskiya ga Ubangiji Allah na kakanninsu, saboda haka ya maishe su kufai kamar yadda kuka gani.

8. Kada ku yi taurin kai kamar yadda kakanninku suka yi, amma ku miƙa kanku ga Ubangiji, ku zo Wuri Mai Tsarki, wanda ya tsarkake har abada, ku bauta wa Ubangiji Allahnku, domin ya huce daga zafin fushin da yake yi da ku.

9. Gama idan kun juyo zuwa ga Ubangiji, 'yan'uwanku da 'ya'yanku za su sami rahamar waɗanda suka kama su, su komo wannan ƙasa. Gama Ubangiji Allahnku mai alheri ne, mai jinƙai, ba zai kawar da fuskarsa daga gare ku ba, idan kun komo gare shi.”

10. Manzannin fa suka tafi gari gari a ƙasar Ifraimu, da ta Manassa, har zuwa Zabaluna, amma suka yi musu dariyar raini, suka yi musu ba'a.

11. Sai mutane kaɗan na Ashiru, da na Manassa, da na Zabaluna suka yi tawali'u, suka zo Urushalima.

Karanta cikakken babi 2 Tar 30