Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Tar 29:12-14-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12-14. Sa'an nan sai Lawiyawa suka tashi,na Kohatawa, Mahat ɗan Amasai, da Yowel ɗan Azariya,na Merari, Kish ɗan Abdi, da Azariya ɗan Yehallelel,na Gershonawa, Yowa ɗan Zimma, da Eden ɗan Yowa,na Elizafan, Shimri da Yehiyel,na Asaf, Zakariya da Mattaniya,na Heman, Yehiyel da Shimai,na Yedutun, Shemaiya da Uzziyel.

15. Sai suka tattara 'yan'uwansu maza, suka tsarkake kansu, suka shiga bisa ga umarnin sarki, bisa ga maganar Ubangiji domin su tsabtace Haikalin Ubangiji.

16. Firistoci fa, suka shiga can cikin Haikalin Ubangiji domin su tsabtace shi. Suka kwaso dukan ƙazantar da yake a Haikalin Ubangiji, suka zuba ta a farfajiyar Haikalin Ubangiji. Sai Lawiyawa suka kwashe, suka zubar a rafin Kidron.

17. A rana ta fari a watan ɗaya suka fara aikin tsarkakewar. A rana ta takwas ga watan suka kai shirayin Ubangiji da aikin, kwana takwas suka ɗauka domin tsabtace Haikalin Ubangiji, a ranar sha shida ga watan ɗaya suka gama.

18. Sai suka tafi wurin sarki Hezekiya suka ce, “Mun tsabtace Haikalin Ubangiji duka, da bagaden hadayar ƙonawa tare da dukan tasoshi, da tukwane, da teburin gurasar ajiyewa da kuma dukan kayayyakin da yake ciki.

19. Dukan kayayyakin da sarki Ahaz ya lalatar a zamaninsa, sa'ad da ya zama marar aminci, mun shirya su mun tsarkake su, suna nan a gaban bagaden Ubangiji.”

Karanta cikakken babi 2 Tar 29