Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Tar 28:1-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ahaz yana da shekara ashirin sa'ad da ya ci sarauta, ya yi shekara goma sha shida yana mulki a Urushalima. Amma shi bai yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji kamar yadda kakansa Dawuda ya yi ba.

2. Ya aikata irin al'amuran da sarakunan Isra'ila suka yi. Ya kuma yi gumakan Ba'al na zubi.

3. Banda haka ma ya ƙona turare a kwarin ɗan Hinnom, ya ƙone 'ya'yansa maza bisa ga ƙazantattun al'adun al'ummai, waɗanda Ubangiji ya kore su daga gaban mutanen Isra'ila.

4. Ya miƙa hadayu, ya ƙona turare a masujadai da a bisa tuddai, da ƙarƙashin kowane itace mai duhuwa.

5. Saboda haka Ubangiji Allahnsa ya bashe shi a hannun Sarkin Suriya. Suka ci shi da yaƙi suka kama mutanensa da yawa, suka kai su Dimashƙu. Aka kuma bashe shi a hannun Sarkin Isra'ila, wanda ya ci shi da yaƙi, ya kashe masa mutane masu yawa.

6. Gama Feka, ɗan Remaliya, ya kashe mutum dubu ɗari da dubu ashirin (120,000) cikin Yahuza a rana ɗaya, dukansu kuwa jarumawa ne, don sun bar bin Ubangiji Allah na kakanninsu.

7. Sai Zikri wani ƙaƙƙarfan mutumin Ifraimu, ya kashe Ma'aseya ɗan sarki, da Azrikam, sarkin fāda, da Elkana wanda yake daga sarki sai shi.

8. Mutanen Isra'ila kuwa suka kwaso 'yan'uwansu da suka kama, mutum dubu ɗari biyu (200,000), mata, da 'ya'ya mata, da 'ya'ya maza. Suka kuma kwaso ganima mai yawan gaske daga gare su. Suka kawo ganimar a Samariya.

9. Amma wani annabin Ubangiji yana nan, sunansa Oded. Shi wannan annabi ya tafi ya taryi rundunar da ta zo Samariya, ya ce musu, “Ga shi, saboda Ubangiji Allah na kakanninku ya yi fushi da Yahuza, ya bashe su a hannunku, ku kuka kashe su da zafin fushi wanda ya kai har sama.

10. Yanzu kuwa kuna niyya ku mai da jama'ar Yahuza da ta Urushalima su zama bayinku mata da maza. Ashe, ku kanku ba ku da waɗansu zunuban da kuka yi wa Ubangiji Allahnku?

11. Yanzu fa, sai ku saurare ni, ku mayar da kamammun da kuka kwaso daga 'yan'uwanku gama Ubangiji yana fushi da ku ƙwarai.”

Karanta cikakken babi 2 Tar 28