Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Tar 23:1-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. A shekara ta bakwai sai Yehoyada ya yi ƙarfin hali, ya haɗa kansa da shugabanni na ɗari ɗari, wato Azariya ɗan Yeroham, da Isma'ilu ɗan Yehohanan, da Azariya ɗan Obed, da Ma'aseya ɗan Adaya, da kuma Elishafat ɗan Zikri.

2. Sai suka shiga ko'ina cikin Yahuza, suka tattaro Lawiyawa daga dukan biranen Yahuza, da shugabannin gidajen kakannin Isra'ila, suka kuwa zo Urushalima.

3. Sai dukan taron suka yi wa sarki alkawari, a Haikalin Allah. Yehoyada ya ce musu, “Wannan shi ne ɗan sarki, sai ya ci sarauta kamar yadda Ubangiji ya faɗa a kan 'ya'yan Dawuda, maza.

4. Ga abin da za ku yi. Sulusin firistoci da Lawiyawa waɗanda ba su aiki ran Asabar, su za su yi tsaron ƙofofi.

5. Sulusinsu kuma a fādar sarki, ɗayan sulusin kuwa a gangare, sauran jama'a duka kuwa a filayen Haikalin Ubangiji.

6. Amma kada kowa ya shiga Haikalin Ubangiji, sai dai firistoci da Lawiyawa masu hidima, su ne za su iya shiga, gama su tsarkaka ne. Amma dukan jama'a su kiyaye shari'a, kada su shiga Wuri Mai Tsarki na Ubangiji.

7. Lawiyawa za su kewaye sarkin, ko wanne da makamansa a hannu, duk wanda ya shiga ɗakin, sai a kashe shi. Su kuma kasance tare da sarki in zai shiga ko zai fita.”

8. Sai Lawiyawa da dukan Yahuza suka yi yadda Yehoyada, firist, ya umarta. Kowannensu ya kawo mutanensa waɗanda ba su aiki ran Asabar, da masu kama aiki ran Asabar, gama Yehoyada, firist, bai sallami ƙungiyoyin ba.

9. Sai Yehoyada firist, ya ba shugabannin māsu da garkuwoyi manya da ƙanana na sarki Dawuda, waɗanda suke cikin Haikalin Allah.

10. Sai ya sa mutane duka su yi tsaron sarki, ko wanne da makami a hannu, tun daga gefen kudu har gefen arewa na Haikalin, da kuma kewaye da bagade da Haikali.

11. Sai ya kawo ɗan sarkin, ya sa masa kambi, ya ba shi dokoki goma, aka yi shela aka ce shi ne sarki. Yehoyada da 'ya'yansa maza suka naɗa shi, suka ce, “Ran sarki ya daɗe!”

12. Sa'ad da Ataliya ta ji sowar mutane, suna ta ribibi suna yabon sarki, sai ta shiga Haikalin Ubangiji wurin jama'a.

13. Sa'ad da ta duba, sai ga sarki yana tsaye wajen ginshiƙin bakin ƙofa, ga shugabanni da masu busa ƙaho kewaye da sarkin. Dukan jama'a suna murna, suna busa ƙaho, mawaƙa kuma da kayan kaɗe-kaɗe da na bushe-bushensu, suna shugabancin shagalin. Sai Ataliya ta yayyage tufafinta ta ce, “Tawaye! Tawaye!”

Karanta cikakken babi 2 Tar 23