Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Tar 20:31-37 Littafi Mai Tsarki (HAU)

31. Yehoshafat ya yi mulkin Yahuza. Yana da shekara talatin da biyar sa'ad da ya ci sarauta. Ya yi mulki a Urushalima shekara ashirin da biyar. Sunan tsohuwarsa Azuba, 'yar Shilhi.

32. Ya bi tafarkin tsohonsa, Asa, bai kuwa kauce ba, ya aikata abin da yake daidai a gaban Ubangiji.

33. Duk da haka ba a kawar da masujadai ba, domin har yanzu mutanen ba su tsayar da zukatansu ga Allahn kakanninsu ba.

34. Sauran ayyukan Yehoshafat, daga farko zuwa ƙarshe, an rubuta su a littafin tarihin Yehu ɗan Hanani, wanda aka rubuta a littafin sarakunan Isra'ila.

35. Bayan haka sai Yehoshafat, Sarkin Yahuza, ya haɗa kai da Ahaziya Sarkin Isra'ila, wanda ya aikata mugunta.

36. Ya haɗa kai da shi, suka gina jiragen ruwa don su riƙa zuwa Tarshish. A Eziyon-geber suka gina jiragen ruwan.

37. Sai Eliyezer ɗan Dodawahu mutumin Maresha, ya yi annabci gāba da Yehoshafat, ya ce, “Saboda ka haɗa kanka da Ahaziya, Ubangiji zai hallaka abin da ka yi.” Don haka jiragen ruwa suka farfashe, suka kāsa tafiya Tarshish.

Karanta cikakken babi 2 Tar 20