Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Tar 20:14-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

14. A tsakiyar taron sai Ruhun Ubangiji ya sauka a kan Yahaziyel ɗan Zakariya, ɗan Benaiya, ɗan Yehiyel, ɗan Mattaniya, Balawe, na 'ya'yan Asaf, maza.

15. Sai Yahaziyel ya ce, “Ku ji, ku dukanku, mutanen Yahuza, da mazaunan Urushalima, da sarki Yehoshafat, ga abin da Ubangiji yake faɗa muku, ‘Kada ku ji tsoro, ko ku razana saboda wannan babban taro, gama wannan yaƙi ba naku ba ne, amma na Allah ne.

16. Ku gangara ku fāɗa musu gobe. Ga shi kuwa, za su haura ta hawan Ziz, za ku tarar da su a ƙarshen kwarin a gabashin jejin Yeruyel.

17. Ba ku za ku yi wannan yaƙi ba, ku dai, ku jā dāga, ku tsaya kurum ku ga nasarar da Ubangiji zai ciwo muku, ya Yahuza da Urushalima. Kada ku ji tsoro ko ku razana, gobe ku fita ku tsaya gāba da su, gama Ubangiji yana tare da ku.’ ”

18. Yehoshafat fa ya sunkuyar da kansa ƙasa, dukan Yahuza da mazaunan Urushalima kuma suka fāɗi ƙasa a gaban Ubangiji, suna masa sujada.

19. Sai Lawiyawa daga Kohatawa da Koratiyawa suka tashi tsaye suka yabi Ubangiji Allah na Isra'ila da babbar murya.

Karanta cikakken babi 2 Tar 20