Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Tar 18:21-31 Littafi Mai Tsarki (HAU)

21. Sai ya ce, ‘Zan tafi in zama ruhun ƙarya a bakin dukan annabawansa.’ Sa'an nan Ubangiji ya ce, ‘To, za ka ruɗe shi har ka yi nasara. Je ka, ka yi haka nan.’

22. “Saboda haka Ubangiji ya sa ruhun ƙarya a bakunan annabawanka, gama Ubangiji ya faɗa, masifa za ta same ka.”

23. Sai Zadakiya ɗan Kena'ana, ya matso ya mari Mikaiya a kumatu ya ce, “Ta wace hanya ruhun Ubangiji ya fita daga gare ni ya zo ya yi magana da kai.”

24. Mikaiya kuwa ya ce, “Za ka gani a ranar da ka shiga ƙuryar ɗaki na can ciki don ɓuya.”

25. Sai Sarkin Isra'ila ya ce, “Ku kama Mikaiya, ku komar da shi wurin Amon mai mulkin birnin, da yarima Yowash.

26. Ku ce, ‘Sarki ya ce ku sa wannan mutum a kurkuku, ku ciyar da shi da ɗan abinci da ruwa kaɗan har in komo lafiya.’ ”

27. Sai Mikaiya ya ce, “Idan har ka komo lafiya, wato Ubangiji bai yi magana da ni ba ke nan.” Sai ya ce, “Ku ji, ya ku jama'a duka.”

28. Sarkin Isra'ila fa, da Yehoshafat Sarkin Yahuza, suka haura zuwa Ramot-gileyad.

29. Sarkin Isra'ila ya ce wa Yehoshafat, “Zan ɓad da kama, in shiga yaƙi, amma kai, sai ka sa rigunanka.” Sarkin Isra'ila kuwa ya ɓad da kama, suka shiga yaƙi.

30. Sarkin Suriya ya umarci shugabannin karusansa, ya ce, “Kada ku yi yaƙi da yaro ko babba, sai dai da Sarkin Isra'ila, shi kaɗai.”

31. Sa'ad da shugabannin karusai suka ga Yehoshafat, suka ce, “Wannan ne Sarkin Isra'ila,” sai suka juya suka yi yaƙi da shi. Amma Yehoshafat ya yi kururuwa, Ubangiji Allah ya kuɓutar da shi, Allah kuwa ya kawar da su daga gare shi.

Karanta cikakken babi 2 Tar 18