Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Tar 14:8-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Sarki Asa kuwa yana da soja dubu ɗari uku (300,000) a Yahuza, ko wanne yana da kutufani da māshi, yana da soja dubu ɗari biyu da dubu tamanin (280,000) daga Biliyaminu, 'yan baka ko wanne da garkuwarsa. Dukansu manyan jarumawa ne.

9. Sai Zera mutumin Habasha ya zo da soja zambar dubu (1,000,000) da karusa ɗari uku har Maresha, don ya yi yaƙi da su.

10. Don haka sai Asa ya fito ya gamu da shi, suka kuwa jā dāga a kwarin Zefata a Maresha.

11. Asa kuwa ya yi kuka ga Ubangiji Allahnsa, ya ce, “Ya Ubangiji, ba wani mai taimako kamarka, wanda zai yi taimako sa'ad da mai ƙarfi zai kara da marar ƙarfi, ka taimake mu, ya Ubangiji Allahnmu, gama a gare ka muke dogara, da sunanka kuma muka zo don mu yi yaƙi da wannan babbar runduna. Ya Ubangiji, kai ne Allahnmu, kada ka bar mutum ya rinjayi jama'arka.”

12. Ubangiji kuwa ya fatattaki Habashawa a gaban Asa da Yahuza, Habashawa kuwa suka gudu.

13. Sai Asa da jama'ar da suke tare da shi, suka runtume su har zuwa Gerar. Habashawa suka fāɗi duka, ko ɗaya, ba wanda ya ragu da rai, gama an ragargaza su a gaban Ubangiji da gaban sojojin. Mutane suka kwashe ganima mai yawa gaske.

14. Suka hallaka dukan birane da suke kewaye da Gerar, gama tsoron Ubangiji ya kama su. Suka washe dukan biranen, gama biranen suna cike da ganima.

15. Suka kware alfarwan masu kiwon dabbobi, suka kora tumaki, da raƙuma masu yawan gaske. Sa'an nan suka komo Urushalima.

Karanta cikakken babi 2 Tar 14