Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Tar 13:15-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. Mutanen Yahuza suka yi kūwwar yaƙi. Da suka yi kuwwar yaƙin sai Ubangiji ya sa Yerobowam da dukan jama'ar Isra'ila su gudu a gaban Abaija da Yahuza.

16. Mutanen Isra'ila kuwa suka gudu a gaban Yahuza, Allah ya bashe su a hannunsa.

17. Abaija fa, da jama'arsa suka karkashe su, mugun kisa. Mutum dubu ɗari biyar (500,000) zaɓaɓɓu na Isra'ila, aka karkashe.

18. Haka kuwa aka ci nasara a kan mutanen Isra'ila a wannan lokaci. Mutanen Yahuza sun yi rinjaye saboda sun dogara ga Ubangiji, Allah na kakanninsu.

19. Abaija ya runtumi Yerobowam, ya ƙwace masa waɗansu birane, wato Betel tare da ƙauyukanta, da Yeshana tare da ƙauyukanta, da kuma Efron tare da ƙauyukanta.

20. Mulkin Yerobowam bai ƙara farfaɗowa a zamanin Abaija ba. Ubangiji kuma ya bugi Yerobowam, ya mutu.

21. Amma Abaija ya ƙasaita, ya auro mata goma sha huɗu, ya haifi 'ya'ya maza ashirin da biyu, da 'ya'ya mata goma sha shida.

22. Sauran ayyukan Abaija, da al'amuransa, da jawabansa, an rubuta su a littafin tarihin annabi Iddo.

Karanta cikakken babi 2 Tar 13