Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Tar 12:9-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Sai Shishak Sarkin Masar ya zo ya fāɗa wa Urushalima da yaƙi, ya kuwa kwashe dukiyoyin da suke cikin Haikalin Ubangiji, da na fādar sarki, ya yi musu ƙaƙaf. Ya kuma kwashe garkuwoyi na zinariya, waɗanda Sulemanu ya yi.

10. Sai sarki Rehobowam ya ƙera garkuwoyin tagulla a madadin na zinariya, ya sa su a hannun shugabannin matsara, masu tsaron gidan sarki.

11. A duk lokacin da sarki ya shiga Haikalin Ubangiji, sai matsara su kawo su, daga baya kuma su maishe su a ɗakin matsaran.

12. Da sarki Rehobowam ya ƙasƙantar da kansa, sai fushin Ubangiji ya huce, don haka bai sa aka hallaka shi ƙaƙaf ba, har ma halin zama a ƙasar Yahuza ya yi kyau.

13. Sarki Rehobowam kuwa ya kafa mulkinsa sosai a Urushalima, yana da shekara arba'in da ɗaya da haihuwa ya ci sarauta, ya yi mulki shekara goma sha bakwai a Urushalima, birnin da Ubangiji ya zaɓa daga dukan kabilan Isra'ila domin ya sa sunansa a wurin. Sunan tsohuwar Rehobowam Na'ama, Ba'ammoniya.

14. Amma ya aikata mugunta domin bai nemi Ubangiji a zuciyarsa ba.

15. Ayyukan Rehobowam, daga farko har zuwa ƙarshe an rubuta su a littafin tarihin annabi Shemaiya, da na Iddo maigani. Kullum yaƙi ne tsakanin Rehobowam da Yerobowam.

16. Rehobowam fa ya rasu, aka binne shi a birnin Dawuda. Abaija ɗansa ya gāji gadon sarautarsa.

Karanta cikakken babi 2 Tar 12