Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Tar 1:1-3 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sulemanu ɗan Dawuda ya kahu sosai cikin mulkinsa, gama Ubangiji Allahnsa yana tare da shi, Ubangiji kuwa ya sa shi ya zama mashahuri.

2. Sulemanu ya yi magana da dukan manya, wato shugabannin dubu dubu, da na ɗari ɗari, da alƙalai, da dukan shugabanni na Isra'ila, wato shugabannin gidajen kakanni.

3. Sa'an nan Sulemanu da dukan waɗanda suke tare da shi, suka tafi masujadar da take a Gibeyon, gama alfarwar sujada ta Allah, wadda Musa, bawan Ubangiji ya yi a jeji, tana can.

Karanta cikakken babi 2 Tar 1