Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sar 6:12-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Ɗaya daga cikin fādawan ya ce, “A'a, ranka ya daɗe, sarki, ai, annabi Elisha ne wanda yake cikin Isra'ila, yake faɗa wa Sarkin Isra'ila maganar da kake faɗa a ɗakin kwananka.”

13. Sai ya ce, “Ku tafi, ku ga inda yake don in aika a kamo shi.” Aka faɗa masa, cewa a Dotan yake.

14. Sai ya aika da dawakai, da karusai, da sojoji da yawa. Suka tafi da dare suka kewaye garin.

15. Da baran annabi Elisha ya tashi da sassafe, ya fita waje, sai ga sojoji, da dawakai, da karusai sun kewaye gari. Sai baran ya ce, “Wayyo, maigidana! Me za mu yi?”

16. Elisha kuwa ya ce masa, “Kada ka ji tsoro gama waɗanda suke tare da mu, sun fi waɗanda suke tare da su yawa.”

17. Sa'an nan Elisha ya yi addu'a ya ce, “Ya Ubangiji, ka buɗe idanunsa ya gani.” Ubangiji kuwa ya buɗe idanun saurayin, sai ga dutsen cike da dawakai da karusan wuta kewaye da Elisha.

18. Da Suriyawa suka gangaro wurinsa, sai Elisha ya yi addu'a ga Ubangiji, ya ce, “Ina roƙonka, ka bugi mutanen nan da makanta.” Ubangiji kuwa ya buge su da makanta bisa ga addu'ar Elisha.

19. Sa'an nan Elisha ya ce musu, “Wannan ba ita ce hanyar ba, ba kuma gari ke nan ba, ku bi ni, ni kuwa in kai ku wurin mutumin da kuke nema.” Sai ya kai su Samariya.

20. Da shigarsu Samariya, sai Elisha, ya ce, “Ya Ubangiji, ka buɗe idanun mutanen nan su gani.” Ubangiji kuwa ya buɗe idanunsu, suka gani, ashe, suna tsakiyar Samariya ne.

21. Da Sarkin Isra'ila ya gan su, sai ya ce wa Elisha, “Ya mai girma, in karkashe su? In karkashe su?”

Karanta cikakken babi 2 Sar 6