Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sar 25:24-30 Littafi Mai Tsarki (HAU)

24. Sai Gedaliya ya rantse musu, su da mutanensu, cewa kada su ji tsoron barorin Kaldiyawa, su zauna a ƙasar, su bauta wa Sarkin Babila, haka zai fi zamar musu alheri.

25. Amma a watan bakwai, sai Isma'ilu ɗan Netaniya, wato jikan Elishama, daga gidan sarauta, ya zo tare da mutum goma ya fāda wa Gedaliya, ya kashe shi tare da Yahudawa da Kaldiyawa da suke tare da shi a Mizfa.

26. Sai dukan mutane, manya da ƙanana, da shugabannin mayaƙa, suka tashi, suka gudu zuwa Masar, gama sun ji tsoron Kaldiyawa.

27. A rana ta ashirin da bakwai ga watan goma sha biyu, a shekara ta talatin da bakwai ta ɗaurin Yekoniya Sarkin Yahuda, sai Ewil-merodak da ya zama Sarkin Babila ya yi wa Yekoniya alheri, ya sake shi a shekarar da ya ci sarautar.

28. Ya yi masa magana mai kyau, ya kuma ba shi matsayi fiye da sarakunan da suke tare da shi a Babila.

29. Sai Yekoniya ya tuɓe tufafinsa na kurkuku. Kowace rana kuwa yakan ci abinci a teburin sarki har muddin ransa.

30. Sarki kuma ya yanka masa kuɗin da za a dinga ba shi, kowace rana muddin ransa.

Karanta cikakken babi 2 Sar 25