Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sar 24:13-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. ya kuma kwashe dukan dukiyar da take cikin Haikalin Ubangiji, da dukiyar da take cikin gidan sarki. Sai ya farfashe tasoshin zinariya da suke cikin Haikalin Ubangiji, waɗanda Sulemanu Sarkin Isra'ila, ya yi. Ya aikata abin da Ubangiji ya riga ya faɗa.

14. Nebukadnezzar ya kwashe dukan mutanen Urushalima, da dukan hakimai da dukan jarumawa, da masu sana'a, da maƙera, har sun kai dubu goma (10,000). Ba wanda ya ragu sai dai matalautan ƙasar.

15. Ya tafi da Yekoniya a Babila, shi da tsohuwarsa, da fādawansa, da masu maƙami na ƙasar.

16. Sarkin Babila ya kai kamammu Babila, wato jarumawa dubu bakwai (7,000), masu sana'a da maƙera dubu ɗaya (1,000), dukansu ƙarfafa ne, sun isa zuwa yaƙi.

17. Sai Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ya naɗa Mattaniya ɗan'uwan tsohon Yekoniya sarki a maimakon Yekoniya sa'an nan ya ba shi suna Zadakiya.

18. Zadakiya yana da shekara ashirin da ɗaya sa'ad da ya ci sarauta. Ya yi mulki a Urushalima shekara goma sha ɗaya. Sunan tsohuwarsa Hamutal, 'yar Irmiya, mutumin Libna.

Karanta cikakken babi 2 Sar 24