Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sar 23:25-37 Littafi Mai Tsarki (HAU)

25. A gabansa, ko bayansa ba wani sarki kamarsa, wanda ya juyo ga Ubangiji da zuciya ɗaya da dukan ransa, da dukan ƙarfinsa domin ya bi dukan dokokin Musa.

26. Duk da haka Ubangiji bai huce daga fushinsa mai zafi da yake yi da jama'ar Yahuza ba, saboda yawan tsokanar da Manassa ya yi masa.

27. Ubangiji kuwa ya ce, “Zan kawar da jama'ar Yahuza daga gabana kamar yadda na kawar da jama'ar Isra'ila. Zan yi watsi da birnin nan da na zaɓa, wato Urushalima, da Haikalin da na ce sunana zai kasance a wurin.”

28. Sauran ayyukan Yosiya da dukan abin da ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Yahuza.

29. A zamaninsa Fir'auna-neko, Sarkin Masar, ya tafi ya tasar wa Sarkin Assuriya da yaƙi a Kogin Yufiretis. Sarki Yosiya kuwa ya yi ƙoƙari ya hana shi wucewa, sa'ad da Fir'auna-neko ya gan shi, sai ya kashe shi a filin yaƙi a Magiddo.

30. Fādawansa kuwa suka ɗauko gawarsa a karusa daga Magiddo, suka kawo Urushalima, suka binne a kabarinsa.Sai jama'ar ƙasa suka naɗa Yehowahaz ɗan Yosiya sarki a matsayin tsohonsa.

31. Yehowahaz yana da shekara ashirin da uku sa'ad da ya ci sarauta. Ya yi mulki wata uku a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Hamutal 'yar Irmiya na Libna.

32. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji kamar yadda kakanninsa suka yi.

33. Fir'auna-neko ya sa shi a kurkuku a Ribla a ƙasar Hamat, don kada ya yi mulki a Urushalima. Ya kuma sa ƙasar ta riƙa ba da gandu, wato haraji, talanti ɗari na azurfa da talanti guda na zinariya.

34. Sai Fir'auna-neko ya sarautar da Eliyakim ɗan Yosiya a matsayin tsohonsa. Ya sāke masa suna ya sa masa suna Yehoyakim. Ya ɗauki Yehowahaz ya tafi da shi Masar, can ya mutu.

35. Yehoyakim yakan ba Fir'auna azurfa da zinariya, ya kuwa sa wa ƙasar haraji don ya sami kuɗin da Fir'auna ya umarta. Ya tilasta wa kowa ya biya azurfa da zinariya bisa ga yadda ya sa masa don ya ba Fir'auna-neko.

36. Yehoyakim yana da shekara ashirin da biyar sa'ad da ya ci sarauta. Ya yi mulki shekara goma sha ɗaya a Urushalima. Sunan tsohuwarsa kuwa Zebida, 'yar Fediya mutumin Ruma.

37. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji kamar yadda dukan kakanninsa suka yi.

Karanta cikakken babi 2 Sar 23