Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sar 23:20-26 Littafi Mai Tsarki (HAU)

20. Ya kuma karkashe dukan firistocin matsafai na kan tuddai a bisa bagadan da suke can. Ya ƙone ƙasusuwansu a bisa bagadan. Sa'an nan ya komo Urushalima.

21. Sarki Yosiya kuwa ya umarci dukan mutane, ya ce, “Ku kiyaye Idin Ƙetarewa ga Ubangiji Allahnku kamar yadda aka rubuta a littafin alkawari.”

22. Gama ba a ƙara kiyaye Idin Ƙetarewa ba tun daga zamanin hakimai waɗanda suka yi hukuncin Isra'ila, ko a zamanin sarakunan Isra'ila da na Yahuza,

23. sai dai a shekara ta goma sha takwas ta sarautar sarki Yosiya an kiyaye Idin Ƙetarewa ɗin nan ga Ubangiji a Urushalima.

24. Yosiya kuma ya kori dukan masu mabiya, da masu maita, da kawunan gidaje, da gumaka, da dukan abubuwa masu banƙyama da ake gani a ƙasar Yahuza, da a Urushalima, don ya sa maganar dokokin da aka rubuta a littafin da Hilkiya firist ya tarar a Haikalin Ubangiji ta kahu.

25. A gabansa, ko bayansa ba wani sarki kamarsa, wanda ya juyo ga Ubangiji da zuciya ɗaya da dukan ransa, da dukan ƙarfinsa domin ya bi dukan dokokin Musa.

26. Duk da haka Ubangiji bai huce daga fushinsa mai zafi da yake yi da jama'ar Yahuza ba, saboda yawan tsokanar da Manassa ya yi masa.

Karanta cikakken babi 2 Sar 23