Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sar 23:2-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. Sa'an nan ya haura zuwa Haikalin Ubangiji tare da dukan jama'ar Yahuza, da dukan mazaunan Urushalima, da firistoci, da annabawa, da jama'a duka, ƙanana da manya. Sai ya karanta musu dukan maganar littafin alkawarin da aka iske a Haikalin Ubangiji.

3. Sarki ya tsaya kusa da ginshiƙi ya yi alkawari ga Ubangiji, cewa zai bi Ubangiji da zuciya ɗaya, da dukan ransa. Zai kiyaye umarnansa, da farillansa, da dokokinsa, ya bi maganar alkawarin da aka rubuta a littafin. Dukan jama'a kuma suka yi alkawarin.

4. Sa'an nan sarki Yosiya ya umarci Hilkiya, babban firist, da firistoci masu daraja ta biyu, da masu tsaron ƙofa, su fitar da tasoshin da aka yi wa Ba'al, da Ashtoret, da dukan taurarin sama, daga cikin Haikalin Ubangiji. Sai ya ƙone su a bayan Urushalima a saurar Kidron, sa'an nan ya kwashe tokarsu zuwa Betel.

5. Ya kuma tuɓe firistocin gumaka waɗanda sarakunan Yahuza suka naɗa domin su ƙona turare a matsafai na kan tuddai a garuruwan Yahuza, da kewayen Urushalima, da firistoci waɗanda suka ƙona turare ga Ba'al, da rana, da wata, da taurari, da dukan rundunan sama.

6. Sai sarki ya fitar da gunkiyan nan Ashtoret, daga cikin Haikalin Ubangiji a Urushalima, ya kai Kidron, ya ƙone ta a ƙoramar Kidron, ta zama toka, ya kuwa watsar da tokar a makabarta.

7. Ya rurrushe ɗakunan karuwai mata da maza da suke a Haikalin Ubangiji, wato wurin da mata suke saƙa labulan gunkiyar.

8. Ya fitar da dukan firistoci daga cikin garuruwan Yahuza, sa'an nan ya lalatar da matsafai na kan tuddai inda firistoci suka ƙona turare, tun daga Geba har zuwa Biyer-sheba. Ya kuma rurrushe matsafai na kan tuddai waɗanda suke a ƙofofin shiga ƙofar Joshuwa, hakimin birnin, waɗanda suke hagu da ƙofar birnin.

Karanta cikakken babi 2 Sar 23