Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sar 22:16-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. ‘Ga shi, zan aukar da masifa a wurin nan, da a mazaunan wurin, bisa ga dukan maganar littafin nan wanda Sarkin Yahuza ya karanta,

17. domin sun rabu da ni, sun ƙona turare ga gumaka don su tsokane ni in yi fushi da aikin hannuwansu. Saboda haka fushina zai ƙuna a kan wurin nan, ba kuwa zai huce ba.’

18. Amma a kan Sarkin Yahuza, wanda ya aiko ku, ku tambayar masa Ubangiji, ku faɗa masa Ubangiji Allah na Isra'ila ya ce, ‘A kan maganar da ka ji,

19. da yake zuciyarka mai tuba ce, ka kuma ƙasƙantar da kanka a gabana sa'ad da ka ji yadda na yi magana gāba da wannan wuri, da kuma mazaunansa, cewa zai zama kufai da la'ana, kai kuwa ka keta tufafinka, ka yi kuka a gabana, hakika na ji kukanka.

20. Domin haka, ba za ka ga hukuncin da yake zuwa a kan Urushalima ba, za a kai ka cikin kabarinka lafiya.’ ”Mutanen kuwa suka mayar wa sarki Yosiya da wannan magana.

Karanta cikakken babi 2 Sar 22