Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sar 21:17-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. Sauran ayyukan Manassa, da dukan abin da ya aikata, da zunubin da ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Yahuza.

18. Manassa ya mutu, aka binne shi a lambun gidansa a gonar Uzza. Ɗansa Amon ya gāji gadon sarautarsa.

19. Amon yana da shekara ashirin da biyu sa'ad da ya ci sarauta. Ya yi mulki shekara biyu a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Meshullemet, 'yar Haruz na Yotba.

20. Ya aikata mugun abu a gaban Ubangiji kamar yadda tsohonsa, Manassa ya yi.

21. Ya bi halin tsohonsa duka. Ya bauta wa gumakan da tsohonsa ya bauta wa, ya kuma yi musu sujada.

22. Ya rabu da Ubangiji Allah na kakanninsa, bai bi tafarkin Ubangiji ba.

23. Fādawansa kuwa suka ƙulla masa maƙarƙashiya, suka kashe shi a gidansa.

Karanta cikakken babi 2 Sar 21