Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sar 21:12-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. saboda haka ni Ubangiji Allah na Isra'ila, zan aukar wa Urushalima da mutanen Yahuza da masifa irin wadda duk wanda ya ji labarinta, sai ya kusa suma.

13. Zan gwada Urushalima da magwajin Samariya da kuma ma'aunin gidan Ahab. Zan kuma suɗe Urushalima kamar yadda mutum yakan suɗe akushi sa'an nan ya kifar da shi.

14. Zan jefar da ragowar gādona, in bashe su a hannun abokan gāba, za su zama ganima da abin waso ga dukan abokan gābansu,

15. saboda sun aikata mugunta a gabana, suka tsokane ni in yi fushi tun ranar da kakanninsu suka fito daga Masar har wa yau.”

16. Banda wannan kuma Manassa ya kashe adalai har ya cika Urushalima daga wannan gefe zuwa wancan da jininsu, banda zunubin da ya sa mutanen Yahuza su yi, har suka aikata abin da yake mugu a gaban Ubangiji.

17. Sauran ayyukan Manassa, da dukan abin da ya aikata, da zunubin da ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Yahuza.

Karanta cikakken babi 2 Sar 21