Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sar 20:1-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. A waɗannan kwanaki sai Hezekiya ya yi rashin lafiya har yana gab da mutuwa. Sai annabi Ishaya, ɗan Amoz, ya zo wurinsa, ya ce masa, “Ubangiji ya ce, ka kintsa gidanka, gama mutuwa za ka yi, ba za ka warke ba.”

2. Hezekiya kuwa ya juya fuskarsa bango, ya yi roƙo ga Ubangiji, yana cewa,

3. “Ka tuna da ni yanzu, ya Ubangiji, ina roƙonka, da yadda na yi tafiya a gabanka da aminci, da zuciya ɗaya, na aikata abin da yake mai kyau a gabanka.” Sai ya yi ta rusa kuka.

4. Kafin Ishaya ya fita daga filin tsakiyar fādar, sai Ubangiji ya yi magana da shi, ya ce,

5. “Ka koma, ka faɗa wa Hezekiya sarkin jama'ata cewa, ‘Ni Ubangiji Allahn kakanka, Dawuda, na ji roƙonka, na kuma ga hawayenka, saboda haka zan warkar da kai, a rana ta uku kuwa za ka haura zuwa Haikalin Ubangiji.

6. Zan ƙara maka shekara goma sha biyar. Zan kuwa cece ka, kai da wannan birni daga hannun Sarkin Assuriya, zan tsare wannan birni don kaina da kuma don bawana, Dawuda.’ ”

7. Sai Ishaya ya ce, “Ku yi masa farsa da ɓaure, marurun zai warke.”

8. Hezekiya kuwa ya ce wa Ishaya, “Mece ce alama, cewa Ubangiji zai warkar da ni har in haura zuwa Haikalin Ubangiji a rana ta uku?”

9. Sai Ishaya ya ce, “Wannan ita ce alama daga wurin Ubangiji, Ubangiji zai cika alkawarin da ya yi. Ƙaƙa kake so, inuwa ta yi gaba da taki goma, ko kuwa ta yi baya da taki goma?”

Karanta cikakken babi 2 Sar 20