Sai Iliya ya ce wa Elisha, “Ina roƙonka, ka dakata a nan, gama Ubangiji ya aike ni har zuwa Betel.”Amma Elisha ya ce, “Na rantse da Ubangiji da kuma kai kanka, ba zan rabu da kai ba.” Saboda haka suka tafi Betel.